An rantsarda sabon Firayim Ministan kasar Canada Justin Trudeau matakin d a ya kawo karshen mulkin masu ra'ayin mazan jiya na shekaru 10.
Trudeau ya jagoranci jam'iyyarsa mai sassaucin ra'ayi da ake kira LP a takaice. Ta sami gagarumar rinjaye a zaben wakilan majalisar dokokin kasar yayinda ta sami kujeru 184 idan aka kwatanta da kujeru 99 da jam'iyyar tsohon Firayim Minista Steven Harper mai ra'ayin rikau.
Trudeau yabi sawun mahaifinsa wanda ya rigamu gidan gaskiya, wanda ya jagoranci kasar na kusan shekaru 20.
Jim kadan bayan da aka rantsar da shi, Trudeau ya bayyana sunayen ministocinsa, wanda jimlar maza da mata cikin majalisar dai-dai suke.
Ministocin wadanda shekarunsu na haifuwa ya kama daga 35-50, sun yi rantsuwar kama aiki nan take cikin manyan harsunan kasar.