Biyo bayan tafiyar milliyoyin kilomita a cikin sararin samaniya, yau Litinin jirgin hukumar Binciken Sararrin Samaniya ta Amurka NASA, zai sauka cikin duniyar wata da ake kira ‘Red Planet’
Masana dai sun zabi inda suke bukatar jirgin ya sauka a karon farko, tsibirin da suka kira ‘InSight’ sun bayyanar da yanki da cewar, babu yawaitar duwatsu, kuma babu iska mai karfi da zata iya zama barazana ga matukin jirgin.
Jirgin zai dauki tsawon mintuna shida kafun shiga cikin duniyar, mai matsanancin zafi, jirgin da yake mahaukacin gudu zai sauka cikin hankali, kana matukin jirgin zai yi amfani da lema mai saukar angulu wato ‘Parachute’ a turance.
Idan har akayi nasarar saukar jirgin yana iya zama na takwas cikin jerin jiragen da suka ziyarci nahiyar. Shugaban binciken Mr. Tom Hoffman, yace “Gabana na ta faduwa kamar ana buga ganga” tun a watan Mayu na wannan shekarar aka fara wannan aikin.
Idan har jirigin ya sauka lafiya, za ace yayi tafiyar kimanin kilomita milliyan 484, idan kuwa aka samu akasin saukar shi a inda aka shiryas, za’a iya samun babbar matsala.
Yau da misallin 3 na yammacin a nan Amurka akesa ran saukar shi, karfe 9 agogon Najeriya, Nijar, Kamaru, karfe 8 agogon Ghana. Ga duk mai bukatar kallon saukar zai iya ziyartar shafin hukumar inda zasu haska saukar kaitsaye.
Facebook Forum