An sami karin mace-macen ne bayanda shugaba Barack Obama ya aika da karin dubban sojoji zuwa can Afghanistan don su bada talalfi ga rundunar sojan Turai ta NATO a fafatikar da take da ‘yantawayen kasar.
Sai dai kuma yanzu an fara janye da yawa daga wadanan sojojin yayinda ake maida harkokin tsaro a hannun sojan Afghanistan a karkashin wata yarjejeniyar da aka tsaida na cewa dukkan sojojin kasashen ketare zasu fice daga kasar kafin shekarar 2014. To amma soja da ‘yansandan Afghanistan din ne aka fi kashewa tun daga lokacin da aka soma wannan yakin a shekarar 2001.
Daga shekarar 2007 kadai zuwa yau, an hallaka ma’aikatan tsaron kasar sun kai 6,500. Haka kuma Majalisar Dinkin Duniya tace daga 2007 zuwa yanzu, an kashe fararen hulan Afghanistan su ma kamar 13,000.