Manchester United zata ci tarar dan wasan tsakiyarta dan kasar Faransa, Paul Pgoba.
Kungiyar tace Pgoba mai shekaru 25 da haihuwa ya aikata laifi, sakamakon sanya hoto da bai daceba a shafinsa na sada zumunci na yanar gizo Instagram, jim kadan bayan da ta bada sanarwan sallaman kocinta Jose Mourinho, a matsayin mai horas da kungiyar a ranar Talata, wanda hakan na nuni da cewar yana nuna murnar da tafiyar kocin.
Sai dai dan wasan ya cire wannan hoton bayan minti goma da sanyawa a yanar gizo.
Manchester tace yin hakan sam bai dace ba, don haka zata dauki mataki a kan dan wasan domin kafin ya share sama da mutane dubu 64, ne suka ga sakon.
Dangantaka tsakanin Mourinho da Pgoba tayi tsamari musamman a 'yan watananin baya, inda ya kasance bai amfani da dan wasan a wasu muhimman wasanni da Manchester ta buga, domin ko a ranar Lahadin da ta gaba Mourinho bai sanya Pgoba a wasan da Liverpool ta lallasa ta daci 3-1 ba na firimiya lig.
Mourinho shi ne kocin da ya sayo Pgoba daga kungiyar Juventus akan zunzurutun kudi har fam miliyan £89, haka kuma yana daukar fam dubu £300 a duk sati a matsayin albashi.
Facebook Forum