Tun daga kamawar watan Disamba kiristoci a mijami'au ke gudanar da shirye-shirye da suka hada da sanya firanni da wutar lantarki masu launi daban daban da gudanar da addu'o'i.
A cewar Rabaran Benjamin Gaina Yesu Almasihu ya kawo sakon salama ne wa duka bil Adam. Ya yi fatan Allah ya bude idanun mutane su gane cewa samun ceto sai ta wurin Yesu Almasihu. Yesu shi ne sarkin salama kuma dalilin kirsimati ke nan.
Bikin kirsimati na tattare da saye-sayen tufafi da kayan abinci iri-iri. Wata Jimmai Tambaya tace lokacin kirimati lokaci na nuna godiya ga Allah da kuma nuna kauna ga kowa. Yesu Almasihu salama ne saboda haka babu tashin hankali.
Wani malamin addinin musulunci a jihar huduba ya yiwa duka al'umma musamman a lokacin na kirsimati.
Alhaji Saidu Adam Jos yace babban kiran da ya keyi wa kowa a Najeriya domin girman Allah a girmama ra'ayin kowa. A girmama addinin kowa. A kyale mutum ya yi anfani da abun da ya zaba ko ya yi addininsa da abun da ya zaba ba tare da tsangwama ba.
Yace idan kirista suna bikinsu na kirsimati a je ya tsagwamesu ba daidai ba ne. Alhaji Adam ya yi tur da zuwa jefa bamabamai a mijami'u ko masallatai ko wurin taro. Yace saboda haka zasu bada goyon baya ga duk kiristoci su cigaba da addininsu.
Jami'an tsaro sun ja kunnuwan mutane masu neman tada fitina yayin bikin kirsimati da su shiga taitayin jikinsu.
Ga karin bayani.