Yayinda yake magana lokacin kaddamar da baje kolen kiwon lafiya na Abia a Umuahia, Dr. Ogar yace wannan matsayin na nuna cewa mutane da yawa suna rayuwa da wannan kwayar cutar.
Yace wajibi ne mutane su san matsayinsu na cutar kanjamau kuma su yi amfani da hanyoyin kariya wadanda suka hada da kauracewa jima’I ga wadanda basu yi aure ba, amfani da kwaroron roba da kuma kiyaye amfani da abubuwa masu tsini da kaifi da sauransu.
Kwamishinan ya kara da cewa akwai karuwar cututtukan da ba su yaduwa daga mutum zuwa mutum, kamar su ciwon suga da hawan jini wadanda ke kashe fiye da mutane miliyan 36 kowacce shekara a duniya. Dr. Ogar yayi gargadin cewa cututtukan baswa nuna alamu har sai sun kusa yin kisa.
Ya baiyyana cewa mutane miliyon 56 na ‘yan Nijeriya na dauke da hawan jini, kuma mutane na bukatar su duba irin rayuwarsu. Ya kara da cewa halaye kamar su shan taba yana kara hadarin cututtukan zuciya da kansar jinni.
Ya kuma ce kolin lafiya na Abiya, shine na farkon irin shi, an shirya shi ne domin yin koyarwa kan cututtukan da basu yaduwa daga mutum zuwa wani mutumin, kuma yayi kira ga mahallarta suyi amfani da abinda suka koya, domin kiyaye lafiya ya zama matsayi na farko gare mu.