Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Malam Aminu Sabo Dambazau Kan Tasirin Aure Tsakanin Kabilu


A cigaba da tattaunawar mu a game da tasirin auren gamaiyya, wato aure tsakanin kabilu daban daban a fadin duniya, mun sami zantawa da kwararren malami a fannin zamantakewa da halaiyar dan'adam Malam Aminu Sabo Danbazau na jami'ar Bayero da ke birnin Kano inda ya tofa albarkacin bakin sa.

Malamin ya bayyana mana cewa aure tsakanin kabila nada matukar tasiri musamman wajan hada kan al'uma daban daban da ma kasa baki daya. Auren taskanin kabilu daban daban na kara karfafa dankon zumunci tsakani kabilun.

A cewar sa, irin abinda aka dade ana mafarkin ya cigaba da faruwa kenan musamman a Najeriya wanda hakan ma na daya daga cikin dalilan da suka sa har aka kirkiro da bautar kasa da daliban da suka gama jami'a kan yi.

Daga karshe malamin ya yi karin bayani akan yadda al'uma zata sami kanta nan gaba musamman idan jama'arta suka cigaba da auratayya tsakanin su da wasu kabilu daban daban.

Saurari cikakkiyar hirar a dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG