Kasar Saudi Arabiyya ta mayar da martani ga ‘yan majalisar dattawan Amurka akan kawo karshen taimakon da sojojin Amurka ke ba wa Saudiyya a yakin da takeyi a Kasar Yamen, saboda zargin yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman da hannu a kisan dan jarida Jamal Khashoggi.
A wata sanarwa da ta fitar, Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta ce, Masarautar Saudi ta yi Allah wadai da wannan matsaya da ‘yan majalisar Dattawan Amurka su ka dauka akan zargi marar tushe, sannan ta kalubalanci ragowar kasashen waje kan shiga cikin harkokin ta.
A satin da ya gabata ne Majalisar dattawan ta Amurka ta dau wannan matakin wanda tamkar gwalewa ce Shugaban Amurka Donald Trump, bayan da ta kada Kuri’ar dakatar da taimakon da Amurka ta ke bawa Saudiyya a yakin da ta ke yi kasar Yemen.
Facebook Forum