An gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya a Najeriya, musamman a shiyyar arewa maso gabashin kasar da ke fama da tsageran kungiyar Boko Haram.
Taron addu’o'in wanda tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon ya jagoranta, an gudanar da shi ne a wata Majami'a dake Yelwan Kagadama a jihar Bauchi.
Tsohon shugaban, ya ce an shirya wannan taron ne a kasa domin zaburar da 'yan Najeriya, a kuma jajirce kan yi wa kasar addu’a don samun waraka daga matsalolin da suke addabar kasar.
Jawabin mai masaukin baki gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi, ya yaba da wannan yunkuri da mabiya addinin Kirista suka yi, domin rokon Allah ya kawo zaman lafiya a kasar musamman a shiyyar Arewa maso Gabas.
Gwamnan ya ce jihar Bauchi ita ce kofar shiga da fita da ta hada Arewa maso gabas da sauran jihohin da take makwabtaka dasu.
A gefe guda kuma an yaba da umurnin da gwamnatocin jihohin Borno, da Yobe suka bayar, game da fadakar da al’ummar Musulmi kan a yi azumi yau Litinin domin neman zaman lafiya.
A saurari rahoto cikin sauti daga Jihar Bauchi a Najeriya.
Facebook Forum