Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ar Jos Ta Kirkiro Sabbin Magunguna Har Da Na Zazzabin Cizon Sauro


Sauro: Langelange mai ramar keta
Sauro: Langelange mai ramar keta

A wani abin tarihi da aka yi a Jami'ar Jos, an samu nasarar kirkiro wasu muhimman magunguna, ciki har da na cizon sauro da na cizon macizai da dai sauransu.

An yi wani abin tarihi inda Jami’ar Jos ta kirkiro magungunan zazzabin cizon sauro da na cizon maciji da na samun ciki da dai sauransu daga tsiro da danginsu.

Wakiliyarmu Zainab Babaji ta ruwaito Shugaban Jami’ar Furfesa Hayward Babale Mafuyai na tabbatar da wannan cigaban da aka samu. Ya jaddada cewa daga itatuwa aka samo sinadaran sarrafa magungunan. Furfesa Mafuyai, wanda ke magana da ‘yan jarida a zagayowar bikin kafa jami’ar karo na 40, ya kuma ce banda batun kiwon lafiya, Jami’ar ta kuma bullo da wani shiri na sasanta al’ummomin da ba su jituwa da juna tare da taimakon kasar Holland (Netherland) da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Abubakar (ii).

To saidai Furfesa Mafuyai y ace jami’ar na fuskantar wasu matsalolin da su ka hada da rashin isasshen filin fadada jami’ar. Y ace akwai kuma sabbin kwasakwasan da su ka bullo da su da za su kara inganta su muddan su ka samu sukuni.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG