Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ar Jigawa Ta Kulla Kawance da Wasu Jami'o'in Kasashen Waje


Gwamna Mohammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa,
Gwamna Mohammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa,

A duk fadin duniya jami'o'i goma sha bakwai suke cikin wani shiri na musamman na kara ilimi ta musayar dalibai da malamai kuma a Najeriya jami'o'in Jigawa da Bayero ne kawai suke ciki

Banda wadannan jami'o'i guda goma sha bakwai da Jami'ar Jigawa ke cikinsu tana kuma da kawance da jami'o'in wasu kasashe dake nahiyar Asiya.

Mataimakin shugaban Jami'ar Farfasa Abdullahu Yusuf Arbado yace an kebe gurabe na musamman a jami'ar domin dalibai daga makwaftan kasashe. Ya kara da cewa a shekarar karatu ta gaba ne jami'ar zata kafa fannin karatun noma.

Burin da jami'ar ta sa gaba shi ne koyas da kananan malamansu su samu digiri na biyu da ma na uku. Sun hada hannu da Birtaniya domin cimma wannan burin.

Gwamnatin jihar tace ta yiwa jami'ar kyakyawan tanadi domin habakata inji mataimakin gwamnan jihar Barrister Ibrahim Hassan Hadeija. A kasafin kudin wannan shekarar gwamnati ta warewa jami'ar kudi nera biliyan uku saboda kammala wasu ayyuka da gwamnatin ta taras an fara yinsu. Kazalika gwamnati na shirin yin tanadin da zai kai jami'ar koyas da karatun kilita.

Jami'ar zata samar ma jihar ma'aikata da masu iliimin fasaha da kimiya na zamani.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG