Jami’an sojin Korea ta Arewa da makwabciyarta ta Kudu, sun gana a jiya Talata a kauyen Panmunjom, a wani sabon yunkuri na kara dakon zumunci yayin da kasashen biyu ke karfafa dangantakarsu a wani mataki na tsallaka kan iyakokinsu.
Koriyoyin biyu dai sun amince su tattauna kan batun rage yawan dakaru da makamai a yankin nan da babu soji ko makamai.
Tattaunawar ta kasance ne, a yayin da wani babban jami’in Amurka ya ce hotunan tauraron dan adam, sun gano wasu sabbin ayyuka da ake yi a tashar Sanumdong da ta samar da makamai masu linzami na farko da kasar ta mallaka, duk da cewa Amurka na ganawa da hukumomin Pyonyang, kan yadda za su wargaza makaman na nukiliya.
A ranar Litinin, Jaridar Washington Post ta ruwaito wasu jami’ai da a ba a bayyana sunayensu ba, suna cewa akwai alamu Korea ta Arewan na sake gina sabbin makamai masu linzami wadanda ke amfani da mai.
Facebook Forum