Yanzu haka jami’an tara haraji na jumhuriyar Niger sun fara wani yajin aikin kwanaki biyu, wato ranakkun Laraba da Alhamis.
Dalilin shiga wannan yajin aikin kuwa ya biyo bayan wata takardan da ministan kudi, Hasuni Masa’udu yasa wa hannu ne da nufin bada kudaden alawus na alhakin sa-ido ga jami’an baitulmalin kasar da takwarorin su na ma’aikatar kudi.
Wannan ne yasa maaikatan suka ce wannan matakin ya sabawa doka.
Shugaban kungiyar ma’aikatan, Musa Umaru ya shaidawa wakilinmu Sule Mummuni Barma cewa basu san abinda takwarorin nasu suka yi ba da za a basu kashi 55 cikin 100 na kudaden nasu, su kuma da su ne ke tattara kudin ba a fada musu abinda za a basu ba.
Ga Sule Mummuni Barma da karin bayani.
Facebook Forum