Wasu daga cikin manyan jami'o'in ƙasar Amurka, sun yanke hulɗa da kamfanin Huawei, yayin da kamfanin ke fuskantar zargi kan zambar kuɗi da almundahana.
Cikin Jami'o'in da su ka yanke hulɗar, akwai Massachusetts Institute of Technology, Jami'ar Princeton da Jami'ar Califonia da ke Berkeley. Sun ce baza su sake karɓar kuɗi daga kamfanin ba, bisa ga bayanan tuhume-tuhumen da gwamnatin tarayya ke musu, tuhumar da ta haɗa da leƙen asiri.
Makarantun na daga cikin makarantu tara da su ka karɓi kuɗi ɗaga kamfanin, shekaru 6 da su ka wuce. Kuɗin da jim'lar su ya kai dala miliyan goma.
A bayanan da su ka fito daga Hukumar kula da ilimi ta ƙasar Amurka, wadda ta nuna kudin, bai hada da kyautar da ya yi ƙasa da dala dubu ɗari biyu da hamsin ba. A Amurka da sauran wasu kasashe, ba abun mamaki ba ne a ga manyan kamfanoni su bada kuɗaɗe dan inganta lamuran da ya shafi bincike.
Facebook Forum