Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Saudiyya Sun Kashe Wasu Mayaka 8


Yarima Muhammad bin Salman na Saudiyya
Yarima Muhammad bin Salman na Saudiyya

A cigaba da yaki da 'yan ta'adda da sauran 'yan bindiga da kasar Saudiyya ke yi, ta ba da sanarwar cewa sojojjnta sun hallaka wasu mayaka 8 a Qatif wadanda ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne.

Kasar Saudiyya ta ce jami’an tsaronta sun hallaka wasu mutane 8 da ake zarginsu da kasancewa ‘yan ta’adda, a yankin Qatif da ke gabashin kasar.

Ma’aikatar Cikin Gidan Saudiyyan ta ce wadanda ake zargin sun mutu ne a musayar wutar da su ka yi da jami’an tsaron kasar a jiya Asabar a tsibirin Tarot.

Gwamnatin Saudiyya ta ce mutanen sun yi ta shirye-shiryen kai harin ta’addanci.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG