Yayin da musulmai ke shirin fara azumin watan Ramadan na bana, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya bada umurnin dakatar da taruwa a masallatai don tafsir ko kuma dogayen nafilfili na Tarawih da Tahajjud don hana yaduwar cutar coronavirus.
Umurnin na kunshe ne a wata sanarwa da hadakar kungiyoyin musulunci da ake kira Jama'atu Nasril Islam da Sultan din ke jagoranta ta fitar.
Dr. Khalid Aliyu shine sakataren kungiyar wadda shelkwatar ta ke Kaduna, ya bayyana cewa ba a masallaci kadai mutane za su iya gudanar da ibadar su Allah ya karba ba.
Dama gabanin wannan sanarwar manyan kungiyoyin musulunci musamman JIBWIS sun dauki matakin dakatar da tura malamai don gudanar da tafsir.
Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce za a iya isar da sakonni ta hanyar kafafen yada labarai na rediyo, talabijin da yanar gizo.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum