Wadannan 'yan ta'adan cikin gida kamar yadda 'yansandan suka bayyana suna shirya kai hare-hare kan Falasdinawa daga wani wurin da ya zama tamkar mabuyarsu da wurin shirya ta'adanci.
Yahudawan da ake zarga da aikata ta'adancin cikin gida sun fito ne daga yankin West Bank. Jami'an tsaron Shin Bet sun ce 'yan ta'adan sun hada da matasa biyu da wani sojan Israila daya.
Ana zarginsu da jefa bam na wuta da barkonon tsohuwa cikin gidajen Falasdinawa tare da kaiwa direbobi da manoma Falasdinawa hari kodayake babu wanda ya ji wani mugun rauni daga abun da suka aikata.
Jami'an tsaron Shin Bet sun ce wadannan 'yan ta'adan sun samu karfin gwuiwa ne daga yadda yahudawa 'yan kama wuri zauna suka dinga jefa bamabamai cikin gidajen Falasdinawa bara. Lamarin ya kaiga mutuwar Falasdinawa uku da suka hada da wani jariri, dukansu sun kone ne kurmus.
Haka ma jiya Laraba wani fasinja da ya samu rauni makon jiya yayinda aka jefawa wata motar safa bam a birnin Qudus ya rasu.
Wata kungiyar 'yan ta'ada dake Gaza ita ce ta dauki alhakin jefa bam din tana cewa fasinjan dan kungiyarsu ne. Ta kirashi wani gwarzon jarumi. Amma har yanzu jami'an Israila basu tantance mutumin ba. Akwai wasu 20 da suka jikata daga harin.