Kawo yanzu mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a hare-haren bam da wasu suka kai kan babban birnin kasar Indonesia, Jakarta.
Wadanda suka rigamu gidan gaskiya sun hada da maharan biyar kodayake ba'a san adadadin wadanda suka jikata ba saboda mahukuntar kasar basu bada alkalumma ba.
Kungiyar ISIS wadda ta yi ikirarin kafa daular Islama a wasu yankunan Iraqi da Syria da ta mamaye, ta dauki alhakin kai harin na safiyar nan.
Kafin hare-haren dama akwai dama ana tsoron hakan na iya faruwa a kasar ta Indonesia idan aka yi la'akari 'yan kasar da suka shiga mayakan yakin sa kai na ISIS suke komawa gida. Ire-iren wadanda suke dawowa ana zaton su ne zasu soma shirya ta'adanci cikin kasarsu.
Hare-haren na yau su ne na farko tun shekarar 2009 da aka kai kan wasu otel guda biyu.