Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Mota da Ya Kashe Mutane 12 A Jamus


Motar da ta tattaka mutane a birnin Berlin kasar Jamus
Motar da ta tattaka mutane a birnin Berlin kasar Jamus

Kungiyar Islama ta IS ta dauki alhakin kai harin mota da ta kashe akalla mutane 12 kuma ta raunata wasu da dama a wata kasuwar sayarda kayan bukin Krismeti a birnin Berlin na kasar Jamus.

A daren jiya Talata ne kungiyar IS ta dora wannan sanarwa a kan shafin watsa labaranta na yanar gizo na Amaq. Sanarwan tace wannan harin na zaman martani ne na auna mutanen kasashen dake hada kai da kasashen dake yaki da kungiyar.

Sanarwan dai ta zo ne jim kadan bayanda yan sandan Jamus suka sake wani mutumin da aka yi tuhumar yana da hannu a wannan harin da aka kai yammacin Litinin, inda wata babbar motar ta murkushe mutane da dama a wannan kasuwar da yan kasar da baki masu yawon bude ido suke saye-sayen kayan Krismeti.

Babban lauyan gwamnatin Jamus din yace an sake wanda ake wa zargin, dan kasar Pakistan saboda rashin isasshiyar shedar dake nuna ya aikata laifin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG