A yau Asabar Iran ta yi gargadi da kakkausar murya cewa, za ta mayar da mummunan martani ga duk wani mataki da aka dauka, wanda ta kalle shi a matsayin na yunkuri ne a kai mata hari.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Abbas Mousavi, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Tasnim cewa, Iran ba za ta bari a keta mata hakkin da ya shafi na kare kan iyakokinta ba.
“Iran ba za ta yi wata-wata ba wajen mayar da martani ga Amurka muddin ta takale ta," inji Mousavi.
A karshen makon nan ne, wasu rahotannin suka nuna cewa Shugaba Donald Trump ya dakatar da wani harin martani da Amurkan ta yi niyyar kai wa akan Iran, bayan da Iran din ta harbo wani jirgin Amurka mara matuki a ranar Alhamis.
Facebook Forum