A yau Lahadi shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya fadi cewa kasancewar dakarun kasashen waje a kasashen dake yakin tekun Persia zai kawo rashin tsaro a yankin.
“Dakarun kasashen ketare na iya kawo matsala da rashin tsaro ga jama’ar mu da kuma yankin mu,” a cewar Rouhani a wani jawabi da ya yi wanda aka nuna a gidan talabijin din kasar. Shugaban na Iran ya kuma ce ya na so ya gabatar da shirin hadin gwiwar yankin na samar da zaman lafiya a gaban Majalisar Dinkin Duniya.
Jiya Asabar shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta caccaki shirin shugaba Donald Trump na tura karin dakarun sojan kasar da kuma kayayyakinsu na yaki ta sama zuwa Saudiyya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, ta na mai cewa wannan shine yunkurin gwamnatin Trump na baya-baya na yiwa majalisar dokokin kasar danwaken zageye.
Firayin ministan kasar Australia Scott Morrison, wanda ya kai ziyara fadar shugaban Amurka ta White House ranar Jumma’ar da ta gabata, ya ce kasar sa ba zata shiga cikin wata harkar soja ba da Amurka a Iran.
Facebook Forum