Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Na Barazanar Komawa Ga Shirinta Na Nukiliya


Hassan Rouhani
Hassan Rouhani

Kasar Iran ta yi barazanar farfado da shirinta na nukiliya zuwa matakin da ya ke kafin ta rattaba hannu a yarjajjeniyar 2015 da manyan kasashen duniya shida.

“Idan kasashen Turai da Amurka ba su son sauke nauyin da ya rataya a wuyansu … mu ma za mu rage naukar namu nauyin mu kuma maida yanayin zuwa yadda ya ke shekaru hudu da su ka gabata,” abin da kamfanin dillancin labaran kasar Iran na IRNA ya ruwaito mai magana da yawun cibiyar shirin nukiliyar Iran na fadi kenan. Ya kara da cewa, “Wannan matakin bai wuce ka’ida ba. Dalilin haka shi ne a samu damar gwada hanyar diflomasiyya saboda ‘yan daya bangaren su koma hayyacinsu su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Yarjajjeniyar ta 2015 ta tanaji cewa Iran ta rage inganta sinadarin uranium a madadin samun sassaucin takunkumi da za ta yi daga Amurka da sauran kasashe biyar da su rattaba hannu kan yarjajjeniyar - irinsu Burtaniya da China da Faransa da Jamus da kuma Rasha.

Shugaba Trump ya kira yarjajjeniyar “mugun aiki,” sannan ya janye Amurka daga ciki tun bara, sannan ya kuma sake kakaba ma Iran takunkumi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG