Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ingila Zata Ci gaba Da Samun Gurabu 4 A Gasar Zakarun Kulob-Kulob Na Turai


UEFA-logo
UEFA-logo

Firimiya Lig ta kasar Ingila zata ci gaba da kasancewa tana da kulob-kulob guda 4 a gasar cin kofin zakarun kulob na Turai a shekarar 2017 zuwa 2018, a bayan da aka yi waje rod da kulob din Juventus ta kasar Italiya daga wannan gasa ta bana.

Bayern Munich ta Jamus ita ce ta cire Juventus da ci 4-2 a karawarsu ta biyu, watauy ta fitar da ita dsaga cikin wannan gasa da ci 6-4.

Wannan sakamako, mummunan labara ne ga kasar Italiya, wadda ta so ta ture Ingila domin ta zamo ta 3 a cikin jerin kasashen Turai wadanda kungiyoyinsu na Lig-Lig suka fi tabuka abin kirki, abinda zai sa a rage kungiyoyin dake wakiltar Ingila a gasar zakarun kulob na Turai daga guda 4 zuwa guda 3.

Cire Juventus da aka yi daga gasar Zakarun kulob-kulob, da kuma lallasa kungiyar Lazio da Sparta Prague ta yi a daya gasar ta Europa League, sun sanya a yanzu haka kasar Italiya ba ta da wakiliya ko guda daya a manyan wasannin na Turai.

Ingila da kuma firimiya Lig dinta, har yanzu suna da Manchester City a cikin gasar zakarun kulob kulob na Turai, da kuma kungiyar Liverpool a gasar Europa League. Jamus da Spain ne kawai suka fi Ingila yawan kungiyoyin cikin wasannin Turai a wannan kakar kwallon.

XS
SM
MD
LG