Daya daga cikin shafufukan sada zumuntar yanar gizo mallakar kamfanin Facebook na hotuna, 'Instagram' ya ce a ranar Alhamis ya gyara matsalar manhajar shafin wadda ta janyo wani canji na wucin gadi, na yadda shafin ke sauya tsare-tsaren shi.
Matsalar da ta shafi manhajar ta kai ga sa kamfanin gudanar da wani gwaji na yadda mutane ke kallon shafin, da kuma yadda suke iya sarrafa shafin.
Ina mai ba mutane hakuri akan kuskuren da aka samu, domin kuwa wani gwajine da ake yi akan wasu tsirarun mutane, amma abun ya wuce har ya kai ga daukacin mutanen da suka ga sauyin
Sauyin canji ya haifar da damuwa ga ma'abota amfani da shafin, wanda ya kai ga sunata amfani da kafar sadarwar Twitter wajen musayar ra'ayin su dangane da sauyin. Mutane da dama sun kwatanta shafin na instagram da na abokin hamayyarsa na snapchat da cewar yafi shi tsari.
A shekarar da ta gabata ne sabon tsarin na snapchat wanda mutane da dama basu amince da yadda yake ba, ya sha suka da ga ma'abota shafin.
Shugaban kamfanin na instagram Adam Mosseri, ya maida martani ga sakon da mutane ke aikawa a kafar sadarwar twitter da cewar, "ina mai ba mutane hakuri akan kuskuren da aka samu, domin kuwa wani gwajine da ake yi akan wasu tsirarun mutane, amma abun ya wuce har ya kai ga daukacin mutanen da suka ga sauyin"
Facebook Forum