A watan Oktoban bara ne gwamnatin Kano ta kafa wani kwamiti da aka dorawa alhakin bincikar batun yawatar sace-sacen yara a Kano, bayan da aka gano wasu yara guda 9 wadanda aka sace a jihar kuma aka yi safarar su zuwa jihar Anambra da ke kudancin Najeriya, har ma aka sauya musu suna da addini.
Bayan shafe kimanin watannin uku zuwa hudu yana aiki, kwamitin ya mika rahotansa mai kunshe da shawarwari 46 ga gwamnati a cikin watan Maris din bana.
A Juma’ar da ta gabata ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sake kafa wani kwamiti da aka baiwa hurumin aiwatar da shawarwarin da kwamitin bayan ya mikawa gwamnati.
Justice Wada Rano mai ritaya shi ne shugaban kwamitin kuma da-ma shi ne ya jagoranci kwamitin farko da ya gudanar da aikin binciken dangane da batun wadanda ake tuhuma da safara da kuma cinikayyyar yaran nan 9 na Kano a can Anambra.
Sai dai kungiyoyin rajin wanzar da adalci ga wannan batu na sata da kuma cinikin yara a Kano na ganin cewa, matakin kafa kwamitoci ba lallai ya magance wannan matsala ba.
Saurara karin bayani a sauti:
Facebook Forum