Tarihin duniya ba zai cika ba har sai an zayyano irin koma baya da annobar Korona bairos ta haddasar. Mussamman idan aka duba bangaren ilimi. Duk kuwa da cewar kasashen da suka cigaba a duniya, sun fito da wasu sabbin hanyoyin gabatar da karatu.
Idan aka duba kasashen yamma, za'a ga cewar basu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun samar da tsarin gabatar da karatu ta kafafen yanar gizo, inda za'a ga cewar dalibai ba'a barsu a baya ba.
Amma idan aka yi la'akari da 'yan uwan su da ke kasashe masu tasowa, kamar nahiyar Afrika, za'a ga abun ba haka yake ba. Don kuwa a Jamhuriyar Nijar, mahukunta sun dau matakin rufe makarantu na tsawon watanni.
Abun tambaya a nan shine, wane irin hali dalibai zasu shiga a dalilin rufe makarantu? Wadannan da wasu matsaloli ne shirin zai maida hankalin akai, da kuma baiwa mahukunta haske akan hanyoyi da suka kamata su bi don kawo karshen matsalar.
Ana iya saurarar shirin a cikin sauti.