Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Igbo Mazauna Adamawa Na Goyon Bayan Najeriya a Matsayin Kasa Daya


 Shugabannin al'ummar Igbo dake jihar Adamawa sun kira taron manema labarai
Shugabannin al'ummar Igbo dake jihar Adamawa sun kira taron manema labarai

Shugabannin al'ummar Igbo dake zaune a jihar Adamawa sun kira taron manema labarai a Yola fadar gwamnati inda suka sake jaddada goyon bayansu ga Najeriya a matsayin kasa daya

A l’ummar Igbo mazauna jihar Adamawa sun ce ba zasu koma yankunan su ba kuma ba za a raba kasar Najeriya ba duk da tada jijiyar wuya da matasan kudanci da arewacin kasa ke yi kan makomar ta kasa daya.

Wannan ita ce matsayar da al’ummar Igbo suka dauka inji ta bakin shuigaban al’ummar Igbo na jihar Adamawa Igwe Chief Godwin Omenaka da yake wa manema labarai bayani a cibiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen jihar Adamawa.

Igwe Godwin Omenaka ya ce don ya tabbatarwa jama’arsa gamsuwarsa da matakan da gwamnatin jihar Adamawa ta dauka na tsaron lafiya da dukiyoyinsu shi ya sa ya maido da matarsa Yola wadda ta je kasar su domin yi wa ‘yarsu wankana ego saboda ya takawa masu neman maida iyalansu gida birki.

Wani dattijo dan sama da shekaru saba’in da biyar Chief Francis Ogogo da ya share sama da shekara arba’in a Yola fadar jihar Adamawa ya ce ba bu inda zasu je kuma ba shi yiwuwa a raba kasar Najeriya don haka ya ke kira ga al’ummar Igbo su kauda fargaba.

A Jihar Taraba makwabciyar jihar Adamawa shugaban kabilar Igbo Chief Joseph Uchedu kuma mai baiwa gwamna shawara na musamman ya ce sun gamsu da matakan da gwamnatin jiha ta dauka na tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu shi ya sa ba su fargabar komawa yankunansu. Sai dai ya tunatar da gwamna bukatar ta kauda bambancin asali da wariya na bangare da dan Najeriya ya fito tsakanin jama’a.

Wata malamar makaranta Madam Peace Okeke ‘yar kabilar Igbo ta shaidawa Muryar Amurka jihar Taraba gida ce a gareta, kuma yara da take karantarwa sun dauke ta a matsayin uwa ita kuma tamkar ‘ya’ya a gareta don haka inji ta bata ga abinda zai mai da ita yankinsu ba.

A bangaren kungiyar Miyyetti Allah ta kasa reshen jihar Taraba inji ta bakin shugabanta Alhaji Jauro Sahabi suna yi wa matasansu gargadi na kada su yarda a yi anfani da su wajen tada fitina. Kan batun janye kafa da aka ce sun yi na kai shanu kudancin Najeriya, y ace sun yi haka don su yi nazarin yadda lamura ke tafiya a yankin.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG