A karon farko cikin shekaru 35 za'a bude gidan silima a kasar Saudi Arabia. Ana sa ran bude gidan majigin a ranar 18 ga wannan watan.
Kamfanin nan harkokin nishadi mafi girma a duniya AMC ya fada jiya laraba cewa hukumomin kasar Saudiyya sun bashi lasisin bude gidan majigi 40 a manyan biranen kasar 15 cikin shekaru 5 masu zuwa.
Kasar wadda aka sani da masu ra’ayin rikau, suna da wadannan gidajen majigin a shekaru 40 da suka gabata, amma manyan malaman su suka tilasta ganin an rufe su.
Bayanai daga shugaban kanfanin AMC Adam Aron, sun tabbatar cewa gidan majigin ba za a nuna banbancin jinsi ba kamar yadda ake tafiyar da sauran wurare ba, amma akwai wasu lokutta da za'a ware domin nuna fina-finai ga jinsi daya.
Wannan yunkurin na sake bude gidajen silima wani bangare ne na bunkasa tafiya da zamani da yarima Mohammed Bin Salman ke hankoron yi musammmam wajen kashe kudi cikin gida a wannan yanayin na faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.
Dama dai ‘yan kasar ta Saudiyya an sansu da son kallon kafofin yada labarai da shirye shiryen nishadi da al’adun kasashen yammacin duniya. Duk da rufe gidajen silima, 'yan kasar suna kallon fina-finai daga Hollywood, da shirye shiryen talabijin na baya-bayan sosai a gidajen su, kuma abune da suke hira akai sosai.
Facebook Forum