Hukumomin jamhuriyar Nijar sun aika da sakonni ga duk masu fada a ji a duk fadin kasar da suka hada da shugabannin gargajiya da na al’umma su zabura su dauki matakan gaggawa domin ceto ilimin boko daga tabarbarewa.
An zargi wasu shugabannin kungiyoyin ‘yan boko dake zagayawa makarantun birane har ma da na karkara domin hana yara karatu. Wannan na da nasaba da takunsakar da gwamnati da daliban Jami’ar Yamai suka shiga.
Bube Nomau magajin garin Tsarnawa ya ce sun samu sanarwa daga gwammnati akan irin halin da ilimi ya shiga a kasar kuma sanin kowa ne abubuwan da ake ciki. Injishi matsala ce ta taso tsakanin malamai da dalibansu har aka yiwa wani malami batanci da shegantaka. Irin wannan halin ne ya yadu har ya bazu cikin kasar.
A cewar magajin garin lamarin yanzu ya kaiga har wasu akan abun da bai taka kara ya karya ba sai su je makarantu su fitar da yara, su koresu, su hanasu makaranta. Dalili ke nan da gwamnati ta ce ba zata amince da hakan ba kuma zata dauki matakan da suka dace.
A nasu bangaren Malam Ahmed Tahiru magatakardan ofishin gundumar Birnin Konni, yayinda yake ganawa da sarakuna da hakimai da ‘yan majalisar wakilai ya yi masu bayanin umurnin da gwamnati ta basu akan sha’anin ilimin boko. Injishi su kula kada wasu su zo suna fitar da yara daga makarantu suna ji suna gani. Ya zama wajibi a kansu duka su shawo kan matsalar.
Wakilin mai martaba sarkin Konni Alhaji Salisu Sardauna ya yi mamakin tsoma yara kanana da daliban Jami’ar Yamai suka yi cikin matsalarsu da gwamnatin kasar. Ta dalilin hakan ya ja kunnuwan iyaye su yiwa ‘ya’yansu ake jami’a kashedin shiga zanga zanga saboda wai, baa bun da aka turasu yi ba ke nan. Dangane da yin anfani da ‘yan yara kuwa ya ce wajibi ne iyaye su tashi su kare yaran.
Shi ko sarkin Fulani Alhaji Mamman Barde cewa ya yi kada a dauki lamarin da wasa.
Ga rahoton Haruna Mamman da karin bayani
Facebook Forum