Rikicin tsakanin jami'an tsaron da kungiyar IPOB da ke fafutukar kafa kasar Biafra, ya yi sanadiyar asarar kimanin rayuka ashirin da daya a farkon makon da ya gabata.
Kungiyar ta zargi gwamnatin jihar Inugu da rundunar ‘yan sandan jihar da hukumar tsaron farin kaya ta DSS da yin rufa-rufa a kan kashe kashen da aka yi, wani muhimmin batun da ta ce ya kamata hukumomi su fito karara sun bayyana wa duniya takamaiman abin da ya faru a waccan Lahadi.
Shugaban kungiyar Kwamred Emmanuel Omubiko, ya ce idan gwamnatin tarayyar Najeriya taki bincika zargin kashe kashe da aka yi na wadanda ake yiwa kallon mambobin kungiyar IPOB inda ake zargin cewa jami’an tsaro da bude wuta a kan su da kuma kashe kimanin mutum 21, idan ba a dauki mataki don gano gaskiyar lamarin ba wannan zai zubar da martabar Najeriya a idon duniya kana zai nuna Najeriya a matsayin kasar da ta gaza.
Ya ce "wannan batu ka iya shafar huldar Najeriya da wasu kasashe a fannin inganta kare da kuma yin biyayya ga dokokin hakkin ‘yan kasa.”
Shima kakakin kungiyar matasan kabilar Ibo ta “Ohaneze Youth Council” a jihar Abia, Modike Chide Ebere, ya ce su matasa kungiyar Ohaneze na jihar Abia suna hada hannu da majalisa ta kasa wurin yin Allah wadai da wadannan kashe kashe na mambobin IPOB, muna kuma kira ga gwamnatin tarayya da ta binciki batun kana a kori duk wani jami’in tsaron da samu da laifin aikta wannan danyen aiki.
Sai dai wakilin Sashen Hausa Alphonsus Okoroigwe ya yi kokarin jin ta bakin kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Inugu Mallam Ahmad Abdurahman don gano gaskiyar lamarin amma hakar sa bata cimma ruwa ba.
Yanzu Kungiyar “Ohaneze Youth Council” ta ce kwamitin binciken da ta kafa don gano gaskiyar abin da ya faru zai bayyana bayanai da ya tattaro daga shaidu nan bada jimawa ba.
Ga dai rahoton wakilin mu Alphonsus Okoroigwe daga Owere:
Facebook Forum