Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zabe Ta Tabbatar Buhari Ne Ya Lashe Zabe A Hukumance


Independent National Electoral Commission chairman, Attahiru Jega, left, views election documents at the coalition center in Abuja, Nigeria, Monday, March 30, 2015, as votes are collated for last Saturday's elections, in Abuja. In a cliffhanger of an elec
Independent National Electoral Commission chairman, Attahiru Jega, left, views election documents at the coalition center in Abuja, Nigeria, Monday, March 30, 2015, as votes are collated for last Saturday's elections, in Abuja. In a cliffhanger of an elec

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, a hukumance ta ayyana Janal Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasar da akayi ranar Asabar ya kada shugaba Goodluck Jonathan.

Hukumar zaben dai ta tabbatar da sakamakon zaben a safiyar yau Laraba. Tsohon shugaban mulkin soja Janal Muhammdu Buhari, na jam’iyyar adawa ta APC, ya sami nasara kan shugaba Jonathan na jam’iyyar PDP da fiye da kuri’u miliyan uku.

Shugaban hukumar zaben Attahiru Jega, yace Buhari ya sami kuri’u miliyan goma sha biyar da da dubu dari hudu, shi kuma shugaba Jonathan ya sami kuri’u miliyan goma sha biyu da dubu dari tara.

Jiya Talata da dare daya fito filli yadda sakamakon zaben zai kasance, shugaban Goodluck Jonathan, yarda ya sha kaye ya kuma godewa ‘yan Najeriya, saboda damar da suka bashi na yi musu shugabanci.

Shugaba Jonathan yace ya cika alkawarin da ya yi na tabbatar da anyi zabe mai sahihanci. Ya kuma fada cewar duk wanda bai yarda da sakamakon zaben ba, to ya bi dokar da kundin tsarin mulki ya tanada domin kalubalantar zaben a kotu. Domin yace babu wani burin da zai sa ‘dan Najeriya ya rasa ransa.

Jam’iyyar PDP ta shugabanci Najeriya har na tsawon shekaru goma sha shida. Muna da karin bayani kan zaben bayan labaran duniya.

XS
SM
MD
LG