Hukumar kula da wasan kwalon kafa ta nahiyar Turai (UEFA) ta tsaida ranar 21, ga watan Maris na shekarar bana, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan laifin da ta bayyana cewar dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya aikata, a wasan da sukayi nasarar fitarda kungiyar kwallon kafar Atletico Madrid cikin gasar zakarun Turai Uefa (Round 16) daci 3-0.
Kwamitin ladabtarwa na hukumar ta UEFA ya samu dan wasan dan kasar Potugal Cristiano Ronaldo, da laifin nuna salon murna na tsokana ta hanyar kama gabansa, bayan zura kwallaye uku ragar Atletico Madrid.
Kocin Atletico Madrid Diego Simeone, shi ya soma nuna murnar da irin wannan salon a karawarsu ta farko a kasar spain bayan da Atletico ta samu nasara akan Juventus da kwallaye 2-0.
Sai dai shima Kocin na Atletico Madrid Diego Simeone, hukumar ta Uefa taci tararsa kudi har Euro dubu 20, inda yayi sa’ar tsallake hukuncin dakatarwa.
Bayan haka sai gashi, Cristiano Ronaldo ya nuna irin wannan salon murnar na tsokana a matsayin ramuwar gayya, bayan zura kwallaye uku a ragar Atletico, wanda duka kwallaye Ronaldo ne ya cisu abinda yayi sanadin fitar da su baki daya daga gasar zakarun Turai a bana.
Inda ake tsammanin shima Cristiano Ronaldo hukumar ta Uefa bazata haramta masa buga wasu wasanni ba amman zata ci tarar sa.
Facebook Forum