Yau bakwai ga watan Afrilu, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta cika shekaru 70 da kafuwa, sannan rana ce har ila yau da aka ware a matsayin ranar Lafiya ta Duniya.
Hukumar ta WHO, ta jagoranci ayyuka daban-daban na yaki da cututtuka masu saurin kisa, kamar irinsu bakon dauro.
Sannan ta hada kai da sauran sassan Duniya domin yaki da sauran cututtuka da suka hada da cutar shan-inna ta Polio, inda a bara bayanai suka nuna cewa yara 17 ne kadai suka kamu da cutar a duk fadin Duniya.
Sai dai bayanai na nuni da cewa hukumar ta fuskantar kalubale da dama.
Rahotannin sun nuna cewa samun alluran rigakafin cututtuka a wasu yankuna na Duniya ya zama babban kalubale, lamarin da ya sa aka sa taken wannan shekara a matsayin “Health for All” wato samar da Lafiya ga “kowa da kowa.”
“Kusan irin kalubalan da muke gani a ko ina, na da nasaba da yanki, wato wuraren da ake fama da rashin isassun cibiyoyin kiwon Lafiya, ko kuma matsalolin da ke da nasaba da irin tsawon jiran da mutum zai yi kafin ganin likita da kuma rashin isassun likitocin.” Inji James Fitzgerald, jami’i a hukumar ta WHO.
Facebook Forum