Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwastam Ta Samu Nasarori Akan Yaki da Ta'adanci


Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Abdullahi Dikko Inde, tare da wasu manyan jami'an hukumar (Nigerian customs and excise boss, Abdullahi Dikko Inde)
Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Abdullahi Dikko Inde, tare da wasu manyan jami'an hukumar (Nigerian customs and excise boss, Abdullahi Dikko Inde)

Shugaban kungiyar hukumomin kwastan ta duniya ya jinjinawa irin nasarorin da kungiyar ta samu karkashin shugabancin shugaban kwastan ta Najeriya Abdullahi Dikko Nde.

A karkashin shugabancin Abdullahi Dikko Nde ya tabbatar cewa an kawo hadin kai tsakanin hukumomin kwastan na kasashen yammaci da tsakiyar Afirka domin su yi aiki bai daya domin cigaban yankin.

Irin wannan hadin kan yana da mahimmancin gaske a duk wani fafitika na kasuwanci da yaki da matsalokin tsaro domin tabbatar da cewa arziki ya bunkasa a yankin baki daya.

Yanzu dai shugaban kwastan din Najeriya ya sauka daga shugabancin hukumomin kwastan na kasashen yammaci da tsakiyar Afirka. Ya mikawa shugaban kwastan din kasar Kamaru wanda ya gajeshi. Nde yace tuni sun yi duk kokarin da yakamata a yi domin tabbatar da cewa Najeriya ta cigaba da ba kasashen yankin goyon baya ta hanyar bada gudunmawar kayan aiki na motoci da kudade da suke bukata domin aikinsu ya bunkasa ya kuma zamo kafada da kafada da Najeriya.

Abdullahi Diko Nde ya yiwa manema labarai karin bayani akan nasarorin da kungiyar tasu ta samu musamman lokacin da ake fafitikar yaki da ta'adanci da wasu matsalolin tsaro a Najeriya sanadiyar irin goyon bayan da kasashe dake makwaftaka da kasar ke bayar wa. Yace da can kasashen dake makwaftaka da Najeriya suna korafin ba'a tuntubarsu. Amma a watan Maris ya gayyatosu yayin da mai ba shugaban kasa shawara a harkokin tsaro Sambo Dasuki yayi magana dasu.

A taron hukumomin kwastan na Chadi da Niger da Kamaru da Binin suka zauna suka tsara yadda zasu tunkari harkar tsaro. Tun lokacin wannan taron kowace kasa tana gaya masu kokarin da ta keyi dangane da hana ta'adanci da kuma shigowar miyagun kwayoyi. Kasashen sun hada kai kuma suna yin tanadi domin su dakile duk wani abun da ka iya tada hankali. Taron da suka yi shi ya kaiga taron shugabannin kasashen a kasar Faransa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG