Babban jami’in hukumar mai kula da jihohin Adamawa da Taraba Mr, Francis Adetoye ya furta haka lokacin da ya ke bayanin ayukan da hukumar ta gudanar daga watan Junairu zuwa Yulin 2017 a Yola fadar jihar Adamawa.
Jami’in ya ce duk da wadannan matsalolin ta tara kudaden haraji naira miliyan dari daya da goma sha daya da dubu dari bakwai da arba’in da biyar dari uku da goma da sha bakwai da kobo arba’in da uku, yayin da kudin tarar shigowa da motoci ta haramtacciyar hanya ta sami naira miliyan arba’in da biyu da dubu dari bakwai da hamsin da shida adadin da ke nuna karuwar sama da naira miliyan ashirin da shida idan aka kwatanta da bara.
Mr, Francis Adetoye ya fadawa taron manema labarai cewa a wasu lokuta jami’an hukumar da taimako shugabannin gargajiya jami’ansa sukan sha da kyar da mazauna kan iyakokin jihohin tare da hadin bakin masu ayukan fasa kwauri suka nemi hallaka su a bakin aikinsu. Kan batun tara kudin haraji jami’in yayi nuni da karuwa da aka samu bana da alama ce masu fasakwauri basu da mabuya a jihohin biyu.
Bayaga ga kudaden haraji da tara da take tarawa hukumar ta mikawa hukumomin tsaron farar hula ta Civil Defence da hukumar yaki da miyagun kwayoyi da gurbatattun abinci NDLEA jarkoki dari hudu na man fetur da gas da katan daya na miyagun kwayoyi da aka yi niyyar fita da su daga Najeriya zuwa makwabciyar ta Kamaru ta kogin binuwai a kwalekwale mai injuna.
Malam Jamilu Audu na hukumar yaki da miyagun kwayoyi NDLEA ya fada a hirar da ya yi da muryar Amurka cewa hadin kai da ke wanzuwa tsakanin hukumar yaki da fasa kwauri da hukumarsa alama ce ta kyakkyawar dangantaka na yaki da da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa. Shima babban jami’in hukumar tsaro ta farar hula Mal. Ibrahim Meswork tabbaci ya bayar na kamo ‘yan fasakwaurin matukar ba su ketara kan iyakokin Najeriya ba.
Jihohin Adamawa da Taraba suna da hanyoyin sumoga kan iyakokinsu da jamhuriyar Kamaru da masu ayukan fasakwauri ke anfani da su inda a bana aka samu ragowar fasakwauri da kashi talatin da biyar inji hukumar kwastam.
Saurari karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum