Hukumar dake kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta amince da sabuwar dokar takaita yawan ‘yan wasan da kungiyoyi za su rika bayarwa a matsayin aro, zuwa wasu kungiyoyi da kuma rage yawan kudaden da ake baiwa wakilan ‘yan wasa da kungiyoyi a matsayin hakkin aikinsu.
Sabon tsarin hukumar shi ne, a kakar wasa ta badi, 2020/21 adadin ‘yan wasan da kowace kungiya take da damar baiwa wata a matsayin aro, zai koma 8 a maimakon barin dan wasa har sai lokacin da suka ga damar maida shi.
Bayan haka FIFA ta bayyana cewa a kakar wasa ta shekarar 2022/2023 adadin zai koma 'yan wasa 6. FIFA ta bayyana cewar hakan ya zama dole, domin kawo karshen yadda manyan kungiyoyi ke boye ‘yan wasa masu yawa, ta hanyar mika su aro.
A bangaren kudaden da za'a rika biyan (Agent) wakilan ‘yan wasa a matsayin lada kuwa, FIFA tace daga kakar wasa ta shekarar 2020/2021, kungiyoyi ba za su rika biyan wakilansu sama da kashi 10% cikin 100% na jimillar kudaden da suka karba na sayar da ‘yan wasansu ba.
Ta kuma kara da cewar za'a dinga biyansu kashi 3% cikin 100% ne kawai kacal daga cikin jimillar kudaden, sai kuma kwatankwacin kashi 3% na farko
da kungiya mai sayen dan wasa zata biya wakilin.
Facebook Forum