Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar DSS Ta Gayyaci Ghali Umar Na’abba


Tsohon Kakakin Majalisar wakilan Najeriya, Ghali Umar Na'abba (Hoto: Instagram ghalinaabba)
Tsohon Kakakin Majalisar wakilan Najeriya, Ghali Umar Na'abba (Hoto: Instagram ghalinaabba)

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS, ta gayyaci tsohon kakakin Majalisar Wakilan kasar, Ghali Umar Na Abba bayan wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels, matakin da kungiyoyin fararen hula suka nuna rashin gamsuwa akai.

Batun aika sammaci da hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ke yawaita yi a duk lokacin da wani dan Najeriya ya bayyana ra’ayinsa game da muhimman abubuwa da suka shafi kasa ba sabon abu ba ne kamar yadda rahotanni ke nunawa.

Na baya-bayan nan shi ne sammacin da hukumar ta aika wa tsohon kakakin majalisar wakilan kasar, Ghali Umar Na’abba da ke jagorantar wata kungiya mai neman kawo sauyi da ake kira NC Front.

Shugaban kula da sha'anin jama'a na kungiyar ta NC Front, Dr. Yunusa Tanko ya tabbatar da gayyatar da aka yi wa Na'abba a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa an aika masa da sammacin ne bayan furucin da ya yi kan gazawar gwamnatin da shugaba Buhari ke jagoranta tare da bayyana ajandar kungiyarsa na NC Front ta kawo sauyi a kasar gabanin zaben shekarar 2023.

Na'abba ya furta kalaman ne a wata hira da gidan talbijin na Channels ya yi da shi.

A ranar Litinin hukumar ta DSS ta ke so Na'abba ya bayyana.

Babban daraktan kungiyar fafutuka kare hakkin fararen hula ta CISLAC kuma babban wakilin kungiyar transparency international, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce suna wuce gona da iri tare da bata wa gwamnati suna.

Rafsanjani ya kuma kara da cewa wadannan hukumomin na kara bayyanawa al'umma cewa gwamnati ba ta damu da su ba tare da jawo wa gwamnati bakin jini.

Duk kokarin jin ta bakin hukumar DSS bayan tuntubar hadimin hulda da jama’ar hukumar Peter Afunaya ya cutura.

‘Yan Najeriya da dama dai na ci gaba da bayyana rashin gamsuwar su da salon sammaci ko kuma gayyatar da hukumar DSS ta dauka tun da shugaba buhari ya dare kan karagar mulki.

A cikin makon da ya gabata ma hukumar DSS ta aika sammaci ga tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dakta Obadiah Mailafia a kan furucinsa a yayin shirin gidan rediyon Nigeria Info game da ayyukan ‘yan ta’adda.

Mailafia ya yi ikrarin cewa ya samu bayanan sirri daga wasu tubabbun ‘yan Boko Haram cewa, daya daga cikin gwamnonin arewacin Najeriya ke jagorantar kungiyar Boko Haram lamarin da ya kai ga cin tarar gidan rediyon na naira miliyan biyar, saboda zargin yada kalaman ɓatanci.

Saurara karin bayani a sauti daga Halima Abdurra'uf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG