Shugaban Sashen koyar da aikin magani da jinya na jami’ar Bingham a Najeriya Dr. Musa Dankyau, ya bayyana cewa, halin ko in kula da kin sauya rayuwa ke haddasa yaduwar cutar kanjamau a kasar, duk da ci gaban da ake samu a yunkurin yaki da cutar.
Dr. Dankyau wanda yake halartar taron yaki da cutar kanjamau na kasa da kasa da ake gudanarwa a halin yanzu a birnin Washington yace, duk da fadakar da jama’a da samar da magunguna kyauta, da kuma tallafi da ake samu daga cibiyoyin agaji da kasashen duniya, har yanzu cutar tana ci gaba da yaduwa a birane da kauyuka.
A cikin hirarsu da Grace Alheri Abdu, Dr. Dankyau ya bayyana jihohin da aka fi yawan masu dauke da cutar, da dalilan yaduwar cutar a jihohin, ya kuma yi bayani kan ikirarin da wadansu masu aikin jinya da masu maganin gargajiya ke yi cewa suna da maganin kanjamau.
Ga kashin farko na hirar.
Hira Da Dr. Musa Dankyau