A ci gaba da tattaunawa da masu wasannin ba da dariya na kasar Hausa, filin A Bari Ya Huce ya gayyato Aminu Aliyu Baba Kofar Nassarawa Kano, wanda aka fi sani da sunan "Baba Ari" domin yi masa tambayoyi kan tarihin rayuwarsa da yadda aka yi ya shiga cikin wannan sha'ani na wasannin bayar da dariya.
Musamman ma, me ya sa Baba Ari ya rungumi taka rawa irin ta dattijo, kuma ina ma'anar sanya tabaro nau'i nau'i da yake yi a duk lokacin da yake fitowa cikin wani wasa na bayar da dariya?
Wai shin Baba Ari kam tsoho ne da gaske ko kuma dai shiga kawai yake yi a lokacin wasa? A dai dubi hotonsu da mai gabatar da wannan shiri, Ibrahim Alfa Ahmed, a lokacin da suka yi hira a Kano ranar Litinin 13 Yuni 2011.
Nan da makonni biyu za a fara jin wannan hira ta su a cikin filin A Bari ya Huce, amma, Baba Ari yayi magana a kan filin na A Bari ya Huce kansa, wanda ake iya ji a kasa, ko kuma a can saman wannan labari daga gefen dama.
Saurari
Baba Ari Yana Magana Kan Shirin A Bari Ya Huce |
Ga wani bidiyo na Baba Ari tare da Dandolo wanda yazo hira da 'yar Baba Ari.