Hillary Clinton tace “gwamnatin Najeriya taki daukan alhakin dake kanta, na kiyaye rayukan kananan yara mata da maza, da ma manya mata da maza, a arewacin Najeriya a shekarun da suka wuce.”
“Dole sai gwamnatin Najeriya ta karbi taimako – musamman na tattara bayanai, da nemo bayanai, da kuma ilimin gane shirye-shiryen ta’addanci. Dole ne sai kwararrun sojojinsu zasu yi amfani dasu wajen wannan yakin, kuma zasu fi tabukar abun arziki idan suka karbi taimakon da ake basu. Najeriya ta yanke shawarwarori marasa kyau, ba shawarwari masu wahala ba,” a cewar Clinton.
Clinton ta cigaba da cewa “Sun yi wasa da arzikin man fetur dinsu, kuma sun bari cin hanci yayi katutu, har hakan yasa suna asarar wasu yankunansu, saboda baza su yanke shawarwari masu wahala ba.”
“Gwamnatin Najeriya taki tunkarar barazanar, domin takalar muhimmiyar matsalar. Maganar gaskiya, dole sai gwamnatin Najeriya ta zage damste wajen kara duka mutanenta, da kuma tabbatarwa duka yara sun samu damar neman ilimi,” a cewar tsohuwar Sakatariyar.
“Dole sai anyi amfani da duk kayan aiki. Dole ne kowa ya ga wannan a matsayinsa. Cin zarafin bil adama ne sosai, kuma hakan na daga cikin ire-iren wahalhalun da mutane a Najeriya da ma wasu sassan Afirka suke fama da su,” ta fada a fusace.