Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Taraba Hatsarin Mota Ya Halaka Al-Majirai Akalla 12


Wani hadarin mota a Afirka ta kudu
Wani hadarin mota a Afirka ta kudu

Wata motar fasinaja ta take akalla yara almajirai 12 ta jikkata wasu 13 yayin suna wanka a wani tabki.

A Taraba, shaidun gani da ido suka ce motar kamfanin "Sunshine" mai jigilar fasinja, mallakar gwamnatin jihar Adamawa, ta halaka yara almajirai akalla 12, a wani kauyen da ake kira Gorando cikin jihar Taraba.

Al'amarin ya auku ne lokacin da matukin yake kokarin kaucewa ramuka, ko kuma tayarsa ta fashe, sai motar ta kwace ta afkawa yara almajirai, wadanda suke wanka a wani tabki, cikin karamar hukumar Gasol.

Rundunar 'Yansandan jihar Taraba, ta tabbatar da wannan labari, tace tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Da yake tabbatar da haka, kakakin rundunar 'yansandan DSP Joseph Koji, yayi kira ga matuka motoci su rage gudu, kuma su tabbatar da lafiyar motocinsu ako da yaushe.

Mallam Usman wanda yake da tsangaya, yace akalla almajiransa takwas suna daga cikin wadanda suka halaka nan take.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG