"Harkar wasan kwaikwayo baiwa ce daga Allah ni a gareni" in ji Amina Ahmad, wata mai wasan kwaikwayo da harsuna har uku.
Ta kara da cewa tana da burin shiga makarantar koyon wasan kwaikwayo, domin kara sanin dabarun sana’ar amma matsalar kudi da wanda zai taimaka shi ke kawo mata cikas.
Ta bayyana haka ne a yayin da DandalinVOA ya iske su suna hada wani wasan kwaikwayo a Kanon Nijeriya.
Ta ce sana’arta dai ita ce wasan kwaikwayo, domin nishadantarwa da kuma isar da wasu darrusa da suka shafi matsalolin rayuwa na yau da kullum.
Tana mai cewa da zarar an kirata aka ce za’a yi wasan kwaikwayo akan wani batu, ba sai an rubuta mata a rubuce ba, kawai za a gaya mata muna son ki fito akan abu kaza da kaza kwatsam sai batutuwan su zo mata idan suka kamala kuma ya bada ma’ana.
Amina ta ce kimanin shekaru bakwai kenan tana wannan sana’a kuma ta kan yi wasan kwaikwayon ne a harsuna uku, kamar yadda ta fadi tun farko harsunan kuwa sune harshen Hausa da na Turanci da kuma Larabci duk wanda ya zo mata zata iya.
Ta kara da cewa babban abin da zai hana mata ci gaba da karatun koyon harkar wasan kwaikwayo bai wuce rashin madafi ba kasancewar dan kudaden da ta samu tana kula da ‘yayanta guda biyu da mijinta ya rasu ya barta da su .