Wani kakakin gwamnatin kasar Afirka Ta Kudu ya ce tun da aka sake kwantar da Mr.Mandela da jijjifin jiya asabar, shi da kan shi yake numfashi, wato ba da taimakon wata na’ura ba.
Ofishin shugaba Jacob Zuma ya gabatar da sanarwar cewa jumma’a cikin dare ciwon Mr.Mandela ya tsananta, sannan aka dauke shi daga gidan shi zuwa asibiti.
Nelson Mandela, Gogarman yaki da akidar wariya da bambancin launin fata, zai yi shekaru casa’in da biyar ranar goma sha takwas ga watan gobe na yuli, kuma a cikin watan afrilun da ya gabata ma ya yi jinyar ciwon madaukai har tsawon kwanaki goma.
Mr.Mandela ya fara fama da ciwon huhun ne tun lokacin zaman kason shekaru ishirin da bakwai da yayi a zamanin mulkin wariyar launin fata. A ‘yan shekarun nan dai ba a cika ganin Mr. Mandela a bainar jama’a ba, saboda karuwar raunin jiki.