Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Babu Daidaituwa Tsakanin Rasha da Ukraine Akan Iskar Gas


Daga hannun dama Vladimir Putin shugaban Rasha da wasu shugabannin
Daga hannun dama Vladimir Putin shugaban Rasha da wasu shugabannin

Kasashen Rasha, Ukraine da wasu daga nahyar yammacin turai basu daidaita ba akan iskar gas da suke saya daga Rasha

Shuwagabannin makamashi a Ukraine da Rasha da Tarayyar Turai sun gagara cimma dai-daituwa akan farashin iskar gas a ganawar da sukayi a Jiya a birnin Brussels.

Amma an kara shirya wata ganawa ranar 29 ga watan Octoba a wani sabon yunkuri na cimma dai-daituwa, a cewar Kwamishinan makamashi na Tarayyar Turai Guenter Oettinger.

Oettinger ya bayyana karfin gwiwar cewa duka bangarorin biyu zasu cimma dai-daituwa a taron mako mai zuwa da sassa ukun suka shirya a birnin Brussels.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG