Gwamnan ya kuma yi kira ga dakarun da su kara kaimi a yaki da Boko Haram domin kwato wadansu garuruwa da har yanzu suke hannun ‘yan ta’addan musamman ma garuruwan dake yankin tabkin Chadi.
Gwamnan ya yi kiran ne a ranar Litinin yayin da ministan tsaron Najeriya Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya ya kai masa ziyara fadar gwamnatinsa dake garin Maiduguri. Ministan ya kai ziyarar ne tare da manyan jami’an sojojin Najeriya.
Gwamnan Borno ya bayyana damuwarsa kan yadda ake hana al’ummar jiharsa gudanar da harkokin kasuwancin da sunan aikin samar da tsaro, lamarin da ya kai shi ga yin kira ga jami’an tsaron su sake tunani a kan yadda wadansu ke fakewa da tsaro suna cin zarafin jama’a.
Gwamna Zulum ya tabbatarwa manyan jami’an tsaron da ministan cewa hukumomin jihar zasu basu duk taimako da suke bukata wurin kawo karshen yaki da Boko Haram domin al’ummar yanikin su ci gaba da harkokin su kamar yadda suka saba.
Gwamnan ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da irin gudunmuwa da taimako da ya yiwa gwamnati da mutanen jihar Borno haka zalika ya godewa shugabannin sojojin da kokarin da suke yi a wannan yaki da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram.
Ga karin bayani daga wakilinmu a Maiduguri Haruna Dauda:
Facebook Forum