Tun bayan sanarwar shirin gwamnatin jihar Lagos na haramta amfani da babur ko Keke NAPEP a manyan titunan jihar daga ranar daya ga watan Fabarairun shekarar nan ta 2020, jama'a ke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da matakin.
A saboda haka, Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tuntubi Honarable Abbas Tajjudeen, shugaban kwamitin kula da harkokin sufuri a majalisar wakilan Najeriya wanda ya ce samar da wata hanya kafin daukar matakin zai taimaka.
Honarable ya kuma ce ya kamata a duba alfanun matakin da akasinsa ta yadda ba zai kawo koma baya ba a kasar, domin kuwa idan aka duba lamarin ana iya kwatanta shi da abin da hausawa ke cewa "kura gaba baya yaki,” saboda bincike ya nuna cewa akan yi amfani da babura wajen aikata ayyukan ashsha, ciki har da sace-sace, da kai hare-hare, wannan shi ya sa wasu jihohin suka haramta amfani da babur a wasu lokuttan.
Bayan tsaro, akwai batun kare rayukan jama’a. Amma abu mafi sauki a nan, a cewar Tajjudden shine a samar da tsari irin na kasashen da suka ci gaba, wanda zai bada damar a yi wa masu amfani da ababen hawa rajista da kuma tabbatar da cewa sun sami horon da ya dace wajen amfani da babur ko Keke NAPEP.
Honarable Tajjudden ya kuma ce, idan ba a iya samar da tsari mai kyau ba, ana iya komawa gidan jiya saboda matasan da aka haramtawa wannan sana’ar na iya rungumar miyagun sana’o’i don rashin abun yi.
Ya kara da cewa Majalisar wakilan Najeriya na kokarin ganin an samar da hanyoyi masu nagarta a kasar nan da wasu ‘yan shekaru masu zuwa, wannan dalilin ya sa majalisar ta amince Gwamnatin Tarayya ta karbo bashi a kasashen ketare, kuma ana sa ran za a yi amfani da kudaden wajen inganta hanyoyin sufuri, da kammala shirin layin dogo daga kudancin Najeriya zuwa Arewacin kasar don habbaka harkokin kasuwanci.
"Majalisar na aiki tukuru tare da bibiyar yadda aka kashe duk wasu kudade da aka ware don yin ayyukan ci gaban kasa," a cewar Honarable Abbas Tajjudden.
Ana iya sauraran tattaunawar cikin sauti.
Facebook Forum