Karshen ta dai Hamas ta yarda da sabuwar tsagaita wuta a Gaza bisa dalilan jinkai a yau Lahadi, amma Israila ta ce za ta ci gaba da yin ruwan wuta a kan hanyoyin karkashin kasan da 'yan tawaye ke bi su na shiga Israila da makamai da kuma mayaka.
Nan take dai Israila ba ta amsawa sanarwar da Hamas ta gabatar ba. cewa za ta yarda da sabuwar tsagaita wuta kafin Sallar Azumi.
Da farko Hamas ce ta wancakalar da tayin Israila na tsawaita tsagaita wuta a jiya asabar, kuma nan da nan suka ci gaba da fafatawa. Firai Ministan Israila Benjamin Netanyahu ya ce ya lura watakila kasashen duniya za su canza ra'ayi, su juyawa Israila baya game da rikicin na kwanaki 20. Amma duk da haka ya lashi takobin cewa Israila za ta dauki kowane irin matakin da ya zama wajibi ta kare al'ummar ta.