Rahoton kwararrun yasa gwamnatin jihar Yobe da hadin gwiwar ma'aikatar muhalli ta kasa da wasu kasashen Afirka suka kirkiro da wani shiri mai suna Great Green Wall a turance.
Wannan shirin yasa gwamnatin jihar Yobe ta farfado da shirin dashen itatuwa na shekara-shekara har da yin alkawarin inganta dokokin kare muhalli da inganta shirin.
Gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Geidam shi ya bayyana hakan yayin shirin dashen itatuwan na wannan shekarar. Kwamishanan muhalli na jihar Alhaji Idi Barde yace Yobe tana cikin jihohin da hamada ke kara kwararowa lamarin da ya shafi manoman jihar sabili da haka gwamnan ya ba ma'aikatar kudi su sayi bishiyoyi iri-iri su dasa da kiran kowa da kowa a tashi a tsayar da hamada.
Ba Najeriya kadai ba, wasu kasashen goma sha daya sun hadu zasu dasa itatuwa wajen kilomita dubu takwas abun da ya kama daga Guinea zuwa Djibuti. A Najeriya jihohi goma sha daya ke cikin shirin kuma gwamnatin tarayya tayi hobasa. Kamar a Yobe gwamnatin tarayya ta kawo kudi da kayan aiki wanda suka shuka kilomita ashirin da takwas. An killace kilomita ashirin da biyu kana gwamnatin tarayya tayi alkawarin bada kudi a gama killace sauran. Yace gwamnan jihar ya bada kudin haka rijiyar bututu domin kada dashen su mutu.
Ga karin bayani.