Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin Jiragen Ruwa a Girka


Jami’an Gwamnatin kasar Girka sun bada rahoton cewa wasu kananan jiragen ruwan fito biyu dake dauke da dimbin masu kaura sun yi hatsarin kifewa a tsibirin Samos, mutane biyu ne suka halaka.

Dogarawan bakin teku sun bayyana cewar an sami nasarar ceton mutane Talatin da shida amma har yanzu ba’a gano inda wasu mutane talatin suke ba, bayan afkuwar hatsarin safiyar yau Litinin.

Daruruwan ‘yan gudun mafaka dake yawaita cika irin wadannan jiragen ruwan suna halaka ne saboda cunkoson fasinja. Yawancin ‘yan gudun mafakar na fitowa ne daga Asiya da Afirka da yankin gabas na tsakiya, wasu kuma daga kasashen tarayyar Turia.

Hukumomin kasashen Girka, da Italiya da malta suka ce sun sha nanatawa kasashen tarayyar Turai da su kara himma wajen bada gudummawar agaji ga irin wadannan ‘yan gudun mafaka a ruwan tekun Turai.
XS
SM
MD
LG