Manchester United tace zata kara wa dan wasanta Juan Mata tsawan kwanteraginsa a Kungiyar na shekaru Hudu masu zuwa inda da wasu ke ganin sabon kocin Manchester United Jose Mourinho, ba zai tafi dashi a Kungiyar ba.
Jose Mourinho dai shiya sayar da Mata wa kungiyar ta Manchester United lokacin yana Chelsea a shekara ta 2014, Juan Mata dan shekara ashirin da takwas da haihuwa kwanteraginsa zai kare a kungiyar ta Manchester United, a karshen kakar wasan shekara mai zuwa.
Itama Kungiyar Liverpool na shirye shiryen kara wa dan wasanta mai suna Coutinho, tsawon kwanteraginsa har zuwa shekara 2020 wananan dan wasa dai Kungiyoyi da dama irin su Barcelona da PSG na zawarcin sa.
Haka kuma Barcelona taki amincewa da tayin da wata kungiya a kasar China mai suna Lodged tayi wa dan wasanta mai suna Arda Turan a kan kudi Yuro miliyan £50m.